Bayan kwashe kusan watanni biyu ba tare da wasanni a nahiyar Turai ba, an dawo gasar Bundesliga a kasar Jamus, inda kungiyoyi 12 suka kara a tsakaninsu, a cigaba da kakar 2019-2020.
A karawar ta jiya asabar, Borrussia Dortmund ta lallasa Shalke 04 da kwallaye 4-0, Augsburg ta sha kashi a gida da ci 2-1 a hannun Wolfsburg, yayinda wasa tsakanin Dusseldorf da Paderborn ya tashi canjaras.
Sauran wasannin sun nuna cewar RB Leipzig tayi kunnen doki da Freiburg, yayinda Hertha Berlin ta bi Hoffenheim har gida ta doke ta da ci 3-0, kamar yadda Borrussia Monchengladbach tabi Frankfurt har gida ta doke ta da ci 3-1.
Yanzu haka dai ‘yan wasan kungiyoyin kwallon kafa musamman a nahiyar Turai, sun koma fagen atasaye, inda mafi akasari ke sa ran cigaba da wasanni a cikin watan Yuni, ciki har da gasar Premier Ingila wadda ta bayyana 1 ga watan na Yuni a matsayin ranar da wasanninta za su cigaba da gudana.
Sai dai za a rika wasannin kwallon kafar ne ba tare da halartar ‘yan kallo kai tsaye zuwa filayen da fafatawar ke gudana ba, tsarin da zai cigaba da wanzuwa har sai an ga bayan annobar coronavirus.
-RFI Hausa