Gwamnatin Kaduna ta ce jami’an tsaro sun yi nasara gano mutum biyu masu ɗauke da cutar korona da suka tsere bayan sanar da su sakamakon gwajin da aka yi masu.
Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Kaduna na Twitter ta ce kwamishinan lafiya na jihar Dr Amina Mohammad Baloni ta tabbatar da cewa yanzu haka suna cibiyar killace masu cutar korona.
Gwamnatin ta ce tun da aka lalabe mutanen biyu aka rasa ta waya, jami’an tsaro suka bi sawunsu.