‘Yan Najeriya 4,984 aka dawo da su gida bayan sun maƙale a birnin Dubai na haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE), sakamakon annobar Korona.
Galibinsu waɗanda suka maƙale a ƙasar sun tsinci kansu a halin ne sakamakon rufe zirga-zirgar jirage tsakanin ƙasashe domin taƙaita yaɗuwar cutar ta Korona.
Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke Ƙasashen Waje (NIDCOM) ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “Yanzu an yi sawun jirgi 18 ke nan da suka kwaso ‘yan Najeriya 4,984 daga Dubai. Daga ciki Gwamnatin UAE ta biya wa mutum 517 a jirage uku na kamfanin Fly Dubai da wasu 380 a jirgin Emirates Airline”,
Mutum 252 ne daga cikinsu suka iso Najeriya a ranar Asabar inda aka sauke su a Filin Jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.
180 daga cikin waɗanda suka dawo gwamnatin UAE ce ta biya musu kuɗin jirgi, saboda rashin kuɗi a cewar NIDCOM.
Gwamnatin UAE ta ba ‘yan Najeriya da bizarsu ta zama a ƙasar ta ƙare wa’adin 17 ga watan Agusta su baro ƙasarta.
Bayan nan ne gwamnatin Najeriya ta fara yunƙurin tun a makon jiya na ganin ta kwaso su.
NIDCOM ta ce ƙarin ‘yan Najeriya 174 za su baro Dubai a ranar 25 ga Agusta ta jirgin Fly Dubai wanda gwamnatin UAE ta ɗauki nauyi.
Hakan ya kai adadin ‘yan Najeriya da ƙasar ta biya wa kuɗin tikitin jirgi zuwa 1,071 daga Dubai.
A kwanakin baya Shugabar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta buƙaci ‘yan Najeriyan da suka maƙale a Dubai da su yi amfani da damar kwaso sun, su dawo gida.