Daga karshe shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bada kai bori ya hau, inda ya sanya takunkumin fuska a karon farko a bainar jama’a tun bayan barkewar annobar cutar korona.
A baya dai Trump ya ki sanya takunkumi a bainar jama’a, duk da ya ce zai iya sanya wa idan jama’a suka yi yawa kuma ba zai iya bada tazara ba. Sai dai hakan ya sanya jam’iyyar adawa ta Republican ta caccaki Trump akan matakinsa, inda ta ce bai iya shugabancin al’umma ba.
Sai dai Trump daga karshe a ziyarar da ya kai cibiyar kiwon lafiya ta ‘Walter Reed National Military Medical Centre’ dake wajen Washington inda ya gana da sojojin da aka raunata da kuma ma’aikatan lafiya dake fagen daga.
Sai dai Trump bai ambaci cewa ko saboda cutar Korona din ya sanya takunkumin ba, amma ya ce shi bai taba gaba da sanya takunkumin ba. Sai dai ya ce ya yi imanin cewa sanya takunkumi yana da wuri da lokacin da ake sanya shi. “Idan kana asibiti, sanya takunkumi abin da ya kamata ka yi ne.” inji shi.
Ya zuwa ranar Juma’a, cutar Korona a Amurka, ta ci rayukan Amurkawa sama da 134,000, a yayin da akalla miliyan uku suka kamu da cutar a Amurka.