A wannan Larabar Koriya ta Kudu ta bi sahun kasashen da suka umarci bude makarantu domin dalibai su fara daukar darasi a wannan lokaci da hukumomi ke aikin dakile yaduwar cutar corona tsakanin al’umma.
Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar wacce ta bayyana kamuwar mutane 32 da cutar ta corona cikin kwana guda a kasar a karon farko.
Ministar Ilimin kasar Yoo Eun-hae ta bayyana cewar da zarar an samu rahoton kamuwar dalibi guda da cutar ta corona nan take za a rufe makarantar, bayan ta umarci ma’aikatar Ilimin ta girke jami’an lafiya dauke da na’urorin gwaji a kofar makarnatu da kuma sinadarin tsaftace hannu wanda dubban dalibai za su yi amfani dashi kafin shiga azuzuwa domin daukar darasi.
Akalla mutane dubu 11 ne suka kamu da cutar ta corona a kasar ta Koriya ta Kudu tun bayan billar cutar kuma tuni mutane 263 suka riga mu gidan gaskiya.
-DW Hausa