Ma’aikatar tallafawa da jinkai ta gwamnatin tarayya ta bai wa gwamnatin jihar Gombe tallafin buhun shinkafa 1, 800 a wani mataki na ganin an bai wa marasa galihu domin tallafa musu sakamakon killace su da aka yi a gida saboda Korona.
Da yake mika kayayyakin a Gombe a ranar Juma’a, Malam Grema Alhaji, Daraktan sashen tallafawa al’umma na ma’aikatar, ya ce sun tallafawa gwamnatin jihar ne a wani mataki na saukakawa al’umma.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tallafin dai za a bai wa zaurawa ne, da kuma nakasassu da marasa galihu.
Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Gombe, mataimakin gwamnan jihar, Manessah ya mika godiyarsu ga gwamnatin tarayyar, inda ya ce za su raba shinkafar ga wadanda aka bukaci a ba su.