Gwamnatin jihar Filato ta ce za ta maida daukacin almajiran dake jihar zuwa garuruwansu na asali.
Gwamnan jihar Simon Lalong ne ya bayyana hakan, sannan kuma ya sassauta dokar killace jama’ar jihar daga ranar Jumma’a zuwa ranar Lahadi don su samu damar fita sayen kayan abinci kafin a komawa dokar ranar Litinin.
Lalong ya ce gwamnati ta dauki matakin maida almajiran ne saboda barazanar cutar coronavirus.
Muhammadu Dahiru Alaramman wata tsangaya a Jos, ya ce kamata ya yi da gwamnati ta tuntubesu kafin daukar wannan matakin kamar yadda Voa Hausa suka labarto.
Wasu almajiran sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin na maida su jihohinsu.