Gwamnatin tarayya ta sanar da amincewar a bude makarantu ga dalibai da ke shirin ɗaukar jarrabawar kammala karatun firamare da sakandare.
Boss Mustapha ne, ya sanar da haka a jiya Litinin a Abuja, a yayin da kwamitinsa ke yiwa shugaban ƙasa ƙarin haske game da cutar Korona.
Yace Shugaba Buhari ya amince a bude makarantu ga daliban ‘yan aji shida na firamare, da kuma ‘yan aji uku na karamar sakandare da kuma ‘yan aji uku na babbar sakandare da ke shirin jarabawar kammala karatu.
Sai dai ya kara da cewa nan gaba za a sanar da matakan da za a bi wajen bude makarantun.