A ci gaba da sabon mataki da yaƙi da cutar Korona a faɗin Najeriya, gwamnatin tarayya a yau Alhamis bayan rahoton kwamitin yaƙi da cutar Korona na gwamnatin tarayya, gwamnatin ta bada damar buɗe sansanin masu yiwa ƙasa hidima (NYSC).
Dakta Sani Aliyu, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ne ya bayyana hakan, yayin ganawa da manema labarai.
https://dimokuradiyya.com.ng/gwamnatin-tarayya-ta-bada-umarnin-buɗe-makarantu/
Ya kuma buƙaci hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima (NYSC) ta fara shirin buɗe sansanoninta da zarar makarantu sun buɗe.
Ya ce gwamnati na shirin samarwa NYSC da isassun kayan kariya gabanin buɗe sansanonin.
“Muna ƙoƙarin fitar da tsauraran matakan tabbatar da ba a samu ɓullar cutar Korona ba idan aka fara” cewar Aliyu.