Bayan kwashe watanni fiye da uku makarantu na garkame sakamakon mummunar annobar cutar Korona, gwamnatin tarayya ta bayyana wasu sharruda guda shida da kowacce makaranta sai ta bi kafin a kai ga bude ta domin ci gaba da karatu.
Cikin sharuddan da gwamnatin ta bayyana ta ce kowacce makaranta da take son ci gaba da karatu sai ta bi wadannan sharudda kamar haka:
- Samar da wajen wanke hannu
- Yin amfani da na’urar gwajin zafin jiki
- Na’urar kashe kwayoyin cuta a kowacce mashigar makaranta da kuma manyan wurare kamar su, Babbar kofar shiga, dakin kwanan dalibai, dakunan karatu, ofisoshi da sauransu.
- Sannan kowacce makaranta ta yi feshin kashe kwayoyin cuta a harabarta.
- Har wala yau dole ne kowacce makaranta ta kula da tsafta
- Tabbatar da tazara a dakunan karatu da ofisoshi.