Ganin yadda cutar Korona ke daɗa yaɗuwa a ƙasar nan gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 8.49 domin siyo kayan yin gwajin cutar a kasar nan.
A jawabin da ministan kiwon lafiya Osagie Ehinare yayi a wajen taron majalisar zartarwa ta ƙasa a ranar laraba, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda cutar ke daɗa yaɗuwa a faɗin ƙasar nan.
Ya ce siyo waɗannan na’urori zai taimaka wajen aikin daƙile yaɗuwar annobar Korona a duniya.
Osagie ya ce hukumar NCDC za ta buɗe sabbin wurare yin gwajin Korona a duk kananan hukumomin dake kasar nan domin daƙile yaɗuwar cutar.
Sakamakon gwajin cutar Korona da hukumar NCDC ta fitar ranar Laraba ya nuna an samu ƙarin mutane 453 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Laraba.
Yanzu mutum 47,743 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 33,943 sun warke, 956 sun rasu. Sannan kuma zuwa yanzu mutum 13,512 ke ɗauke da cutar a faɗin Najeriya baki ɗaya.