Hakimin Kajuru a jihar Kaduna, Titus Dauda ya kamu da cutar coronavirus.
Basaraken ya shafe kusa mako guda yana fama da zazzabi kafin a kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
A sanarwar da ya fitar da kansa ranar Asabar, hakimin ya ce gwajin da aka yi masa ya nuna ya kamu da cutar sarƙe numfashi ta Korona.
https://dimokuradiyya.com.ng/korona-an-sake-killace-wadanda-suka-tsere-a-kaduna-bayan-gano-su/
“Sakamakon zazzaɓin da na yi fama da shi har na je asibiti aka yi mini gwajin Korona ya fito kuma ya nuna inda dauke da cutar.
“Yanzu ina cibiyar killace masu cutar ta gwamnati ana duba ni. Ina rokon addu’o’inku gare ni da saruan masu cutar”, inji sanarwar.