Gidan Rediyon Jamus ya labarto cewa; Firaministan Italiya Giuseppe Conte ya yi karin haske a game da sassaucin da kasarsa za ta yi na matakan takaita zirga-zirga da gwamnatin ta tanada domin dakile cutar coronavirus.
Giuseppe Conte ya ce daga ranar Litinin mai zuwa shaguna da kantuna za su sake budewa, yayin da wuraran ninkaya da na wasannin motsa jiki sai ranar 25 ga watan Mayu. Kana ya ce a ranar uku ga watan Yuni ‘yan Italiyar za su iya sakewa su je inda suka ga dama babu tsongoma, sannan ya ce ‘yan kasashen waje na Turai za su iya kai ziyara ba tare da an killace su ba.