Ministan matasa da bunkasa harkokin wasanni, Sunday Dare ya raba takunkumin fuska guda dubu biyar a jihar Oyo a wani mataki na taimakawa wajen dakile yaduwar cutar Korona.
Ministan wanda ya samu wakilci mai bashi shawara kan harkokin watsa labarai, John Joshua-Akanji, ya bada wannan gudummawar ne a ofishin tuntuba na jihar Oyo din dake Abuja a ranar Talata.
Ministan ya ce ya bada wannan gudummawar ne domin tallafawa gwamnan a yaki da yake yi da korona a jihar.
Sunday Dare ya ce hanya daya ce kawai na kawo karshen wannan cutar shi ne a hada hannu wajen kawo karshensa tare da bin ka’idojin da masana lafiya suka bayar.