Kamfanin layin wayar salula na MTN da kuma kamfanin waya na Samsung sun raba wayoyin hannu 500 dauke da layukan waya ga ma’aikatan lafiya a fadin kasarnan a wani mataki na taimakawa wajen yaki da cutar korona.
Tobechukwu Okigbo, Jami’in kamfanin na MTN shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce kowanne layin waya na dauke DATA 2GB har na tsawon wata shida.
MTN sun tabbatar da cewa za su raba wa jami’an dake kula da cibiyoyin killace masu cutar korona dake fadin jihohi 36 dake kasarnan ciki harda birnin tarayya Abuja.
“Wannan gudummawar a wani mataki ne na saukaka samunn bayanai a wadannan cibiyoyin, tare da taimakawa gwamnati a matakinta na dakile wannan annobar cutar Korona,” inji Okigbo.
Caden Yu, Manajan Daraktan Samsung ya ce sun yi hakan ne a wani mataki na kamfanin wajen yaki da cutar korona.