Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da mutuwar mutum uku sakamakon cutar korona.
A wata sanarwa da Kakakin gwamnan ya fitar, Muhammad Bello ya ce Gwamna Tambuwal ya ce dukkanin mutum ukun da suka mutu na da wasu cutuka da ke damun su kamar cutar Suga da Asma da hawan jini.
Rahotanni dai na cewa cikin wadanda suka mutu har da mataimakin shugaban jami’ar Usman Danfodio da ke Sakkwato, Farfesa Lawali Abubakar Kwatarkwashi.
Farfesa Kwatarkwashi wanda Malami ne a tsangayar koyar da aikin noma na jami’ar ya rasu ne a daren jiya Talata.