Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an samu ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar Korona har ninki uku tsakanin matasa cikin watanni 5 da suka gabata, inda ta ɗora laifin karuwar akan rashin kiyaye ƙa’idar ba da tazara.
Ta kuma ƙara da cewa, kaso 15% na alƙaluman masu cutar miliyan 6 sun harbu ne tsakanin watan Fabrairu zuwa tsakiyar watan Yuli, kuma ya kasance tsakanin masu shekaru 15 zuwa 24.
Kafin ƙarshen watan Fabrairu, alƙaluman sun kai kaso 4.5%.
A cewar Daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Gheberyesus, “mun sha faɗa kuma za mu sake faɗa cewa matasa ba su tsira daga cutar ba, matasa za su iya harbuwa; matasa za su iya mutuwa kana za su iya yaɗa wa wasu cutar.”
Ya zuwa yanzu aƙalla mutane miliyan 18.5 ke fama da cutar a duk faɗin duniya a cewar Jami’ar John Hopkins.