Bankin Duniya ya amince ya bai wa Nijeriya tallafin dala miliyan 114.28 – kwatankwacin naira biliyan 43 – domin yaƙi da annobar korona musamman a matakin jihohi, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na Nijeriya.
Bankin ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce dala miliyan 100 za ta fito ne daga ƙungiyar International Development Association (IDA), sai kuma miliyan 14.28 da za ta fito daga sashen Pandemic Emergency Financing Facility.
Sanarwar ta kara da cewa; gwamnatin tarayyar Nijeriya za ta bayar da lamuni ga jihohi 36 na ƙasar ciki har da birnin tarayya Abuja ta hanyar tsarin yaƙi da annobar da aka yi wa laƙabi da COVID-19 Preparedness and Response Project (CoPREP).