Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin killace jama’ar Jihar Kano a gidajen su har a tsawon mako biyu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona wacce take yiwa al’ummar jihar Kano da makwabtan jihar barazana.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a yayin jawabi ga al’ummar kasar a daren wannan Litinin din dangane da makomar dokar hana zirga-zirgar da ta shafe wata guda tana aiki a wasu jihohi ciki harda da Legas, Ogun da kuma Abuja.
A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta tura dukkan jami’an da suka dace domin taimakawa jihar fuskantar wannan annobar COVID-19 da ta jefa jama’a cikin halin kunci da kuma rasa rayuka.