Honorabul Sule Adamu ya rasu ne yayin da ake jiran sakamakon gwajin cutar korona da aka yi masa, inda daga baya gwajin ya tabbatar yana dauke da cutar.
Gwamnan jihar Abdullahi Sule ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar ga manema labarai yayin da yake bayani kan halin da ake ciki game da annobar a jihar.
Gwamnatin Nasarawa ta rufe zauren majalisar tare da killace dukkanin ‘yan majalisar da zummar dakile bazuwar cutar a jihar.