Gwamnatin jihar Kebbi ta sanar da mutuwar mutum na farko mai dauke da cutar Korona.
Shugaban dake lura da yaki da cutar a jihar, STF, Alhaji Muhammad Jafaar, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a ranar Asabar a Birnin Kebbi, inda ya ce mutum na biyu da ke dauke da cutar da shekara 60 ne da aka kawo shi daga asibitin koyarwa na Usmanu Dan Fodio dake Sokoto zuwa jihar.
Jafaar, wanda yake shi ne Kwamishinan lafiya na jihar, ya yi bayanin cewa mara lafiyar an gano shi ne a asibitin gwamnatin tarayya wato FMC Birnin Kebbi inda ake lura da shi kan cutar suga da hawan jini kafin Korona ta kama shi.