Sabbin alkaluman hukumomin lafiya sun nuna cewar Turai ta zama nahiya ta farko a duniya da cutar coronavirus ta halaka wa sama da mutane dubu 500, shekara guda bayan barkewar annobar.
Sabon rohoton hukumomin lafiyar wanda gidan Rediyon Faransa suka wallafa ya nuna cewa a halin yanzu jumullar mutane dubu 500 da 69 ne annobar coronavirus ta halaka a nahiyar Turai kadai, daga cikin sama da miliyan 23 da suka kamu da cutar.
Alkalumma sun nuna cewa a tsawon mako guda kadai sama da mutane dubu 37 ne suka mutu a dalilin annobar ta coronavirus a Turan.
Wannan adadi ya sanya Turai zama nahiyar farko da annobar ta halaka mutane sama da rabin miliyan.
Yankin Latin ko kudancin Amurka da Carribean ke biye da Turan da adadin mutane dubu 477 da 404 da cutar ta aika barzahu, sai kuma Amurka da Canada, inda annobar ta lakume rayuka dubu 321, da 287, sai Asiya da ta rasa mutane dubu 208, da 149.