Wata kungiya mai zaman kanta dake tattara alkaluman ‘yan jaridun da suka mutu a sassan duniya, ta ce sama da manema labaran 600 annobar Coronavirus ta halaka daga watan Maris na 2020, zuwa karshen shekarar.
Kungiyar mai suna PEC a takaice tace daga cikin jumillar ‘yan jaridu 602 da annobar ta korona ta aika barzahu a sassan duniya, 303 sun mutu ne a yankin Latin ko Kudancin Amurka kadai, 145 a Asiya, 94 a Turai, 32 a Amurka, sai kuma nahiyar Afrika da cutar ta halakawa manema labarai 28.
A matakin kasashe kuwa, maeman labarai 93 annobar ta Korona ta halaka a Peru, 55 a Brazil, 53 a Indiya, 45 a Mexico, sai 42 a Ecuador.
Bangladesh ta rasa ‘yan jaridu 41, Italiya 37, yayinda manema labarai 31 suka mutu a Amurka bayan kamuwa da cutar Korona.
Sai dai rahoton kungiyar sa idon ta PEC yace ba zai yiwuwa a iya tantance manema labaran da suka mutu suna kan aiki ba.