Kasar Saudiyya ta rubanya harajin kaya sau uku a wani matakin samun kudaden tayar da komadar tattalin arzikin kasar da ya samu koma-baya saboda annobar korona.
Gwamnatin kasar ta ce za ta dakatar da duk alawus-alawus din da ake bai wa ‘yan kasar marasa aikin yi domin tsuke bakin aljihun baitil malin kasar.
Kasar ta Saudiyya dai wadda ta dogara kan arzikin albarkatun man fetir ta fuskanci matsalar tattalin arzikin sakamakon yadda farashin danyen mai ya yi faduwar warwas a kasuwar duniya.
Shekaru biyu kenan dai da kasar ta fito da harajin kayan a wani mataki na rage yawan dogaro ga man fetur.
-Bbc Hausa