Katafaren kamfanin sufurin jiragen sama na British Airways, ya bayyana shirin sallamar ma’aikatansa dubu 12, a karkashin wani shirin gudanar da sauye-sauye a dalilin illar da cutar coronavirus ta yiwa harkokinsa.
Kamfanin IAG da ya mallaki kamfanin na ritish Airways yace yana cigaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan shirin daukar matakin, amma ya bada tabbacin cewar tabbas zai sallami dubban ma’akatan nasa.
Kamfanin yace za a dauki shekaru da dama kafin ya koma gudanar da harkokinsa kamar yadda ya saba bayan shawo kan annobar coronavirus da ta kashe mutane sama da mutane dubu 214 a fadin duniya.
British Airways na da matuka jirage dubu 4 da 500 da masu aiki a cikin jirage dubu 16.
-RFI Hausa