Kungiyar ‘yan canji ta Nijeriya, ABCON a ranar Alhamis ta ce tuni ta wayar da kan membobinta tare da sanar da su matakan da ya kamata su dauka wajen dakile yaduwar cutar Korona da zarar sun dawo bakin aiki.
Alhaji Aminu Gwadabe, shugaban ABCON shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a Legas, inda ya ce tuni ‘yan canjin ke cikin farin cikin dawo wa bakin aiki da kuma tsarin da CBN ta bullo da shi dangane da ci gaba da canjin kudaden waje.
Ya ci gaba da cewa dokar zaman gida na mako 5 da aka kakaba ya sanya canjin kudaden waje a bakar kasuwa ya yi tashi gwauron zabi, inda yanzu Dala 1 take a naira 450.