Makarantu za su koma karatu daga ranar 14 ga watan Satumba a jihar Legas, bayan rufe su sakamakon ɓullar cutar Korona a watan Fabrairu.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar cewa jihar za ta buɗe manyan makarantu a ranar 14 ga watan Satumba, kafin makarantun firarmare da sakandire da akwai yiwuwar buɗe su a ranar 21 ga watan na Satumba.
“Ina farin cikin sanar da cewa za a bar manyan makarantu su buɗe daga ranar 14 ga Satumba, 2020″.
“Game da makarantunmu na firamare da sakandire kuma, muna ƙoƙarin ganin buɗe su a ranar 21 ga watan Satumba, 2020.
https://dimokuradiyya.com.ng/mutum-32-sun-sake-warke-wa-daga-cutar-korona-a-jihar-legas/
“Wannan ba kamar wahayi ba ne, za a iya sauyawa gwargwadon abun da Ma’aikatar Lafiya da ke lura da yadda ake bin matakan kariyar cutar ta lura”, cewar gwamnan.
Tun a watan Maris gwamnati ta rufe makarantu a faɗin tarayyar Najeriya a ƙoƙarin daƙile yaɗuwar annobar Korona, wadda ta fara ɓulla a Jihar Legas a Najeriya.
A ranar 4 ga Agusta aka buɗe makarantu ga dalibai masu rubuta jarbawar kammala sakandire domin rubuta jarabawar WAEC, wanda aka fara a ranar 17 ga wannan wata na Agusta da muke ciki.