Labari mai dadin ji daga kasar Mauritaniya musamman ga al’ummar Musulmi shi ne bayan kwashe mako guda ba a samu sabbin masu dauke da cutar Korona ba a kasar, za a sake bude masallatan Juma’a da kasuwanni a kasar.
Hukumomin kasar sun amince a bude masallatai domin gudanar da sallah, sai dai sun yi kira ga masallata akan su yi dokokin dakile yaduwar cutar Korona da ya hada da bada tazara, sanya takunkumin fuska, kiran da ake ganin wadansu za su yi watsi da shi.
Gwamnatin ta ce duk da haka za ta sassauta dokokin a kasar, tare da bijiro da hanyoyin da za a magance yaduwar cutar a kasar, inda a yanzu za a rika barin ana zuw akasuwa tare da gudanar da sallar Juma’a.
Kafar Africa News ta labarto cewa, wani ma’aikacin gwamnati mai suna Ly Almamy ya ce wannan annobar ya yi matukar takurawa jama’a, ya ce; wannan budewar ya ba su kwarin guiwa, a don haka ya ce za su ci gaba da gudanar da addu’o’i a daidai lokacin da aka bar Musulmai su gudanar da sallolinsu.