Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; sakamakon yaduwar Koronabairos a Nijeriya, hakan ya sanya dole an dakatar da shari’o’i dake kotuna guda 155,757 na shekarar 2019/2020.
Haka zalika adadin shari’o’i 51,983 dake dakon shari’a kuma ake ci gaba da ajiye wadanda ake zargi a gidan gyaran hali, Koronabairos ya dakatar da shari’arsu wanda wannan ke nuni da cewa wadanda suke dauren za su ci gaba da kasancewa a daure a gidajen yarin kasarnan har lokacin da za a magance Koronabairos.
Sai dai a ranar 29 ga watan Maris din 2020, shugaban Buhari, ya bada umurnin dakatar da zirga-zirga a Abuja, Legas da kuma Ogun, akalla na kwana 14 a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona. Inda a ranar 13 ga watan Afrilu aka sake sabunta dokar.
Haka zalika sauran jihohi 36 dake Nijeriya sun ayyana irin na su dokar a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona.