Wata kotun sauraren laifuka dake zamanta a Ikeja a jihar Legas ta yankewa wani matashi mai shekaru 21 a duniya Paul Adesanya, zaman gidan kaso bissa laifin damfarar wata mata mai suna Misis Oluwatoyin Akinwole, mazauniyar Amurka kuɗi Naira Miliyan 36.7.
Wakilin hukumar EFCC ya shaidawa mai shari’a Mojisola Dada cewa matashin ya tura hotunan tsiraicin matar a kafafen sada zumunta, wanda daga bisani matar ta hallaka kanta ta hanyar faɗowa daga babbar gadar Mainland a shekara ta 2017.
Mai shari’a Dada a lokacin da ta ƙarin haske kafin yanke hukunci ta bayyana cewa ana tuhumarsa da aikata laifuka mabanbanta har guda uku.
https://dimokuradiyya.com.ng/majalisa-ta-jinjinawa-efcc-bisa-yaki-da-yan-damfarar-intanet/
“Laifi na farko dana biyu sun jawo an yanke ma hukuncin shekaru bakwai a gidan yari.”
“Laifi na uku sakamakon damfara da kuma sanadin salwantar rayuwar wadda ka damfara ya jawo maka ƙarin shekaru bakwai, dan haka kotu ta yanke maka shekaru goma sha huɗu a gidan yari”.
Daga ƙarshe jami’in hukumar EFCC ya godewa mai shari’a Dada bisa wannan hukunci na adalci da ta yanke.