Gidan Yarin Kaduna a ranar Juma’a 5 ga watan Yunin 2020 ya amshi Sadiq Mustapha wani wanda aka yankewa hukunci kuma gidan Yarin ya ki karbarshi sakamakon fargabar ka da ya yada annobar cutar Korona.
Sadiq wanda aka yankewa hukuncin zaman gidan yarin, a ranar 20 ga watan Mayun 2020 ne, Jami’an EFCC suka kai shi gidan yarin, amma sai ya zama gidan yarin ba su karbe shi ba a wani mataki na kare wadanda suke ciki daga kamuwa da cutar Korona kamar yadda shugaban gidan yarin, Sanusi Danmusa ya tabbatar.
Sadiq Mustapha an maishe da shi ma’ajiyar EFCC inda ya kwashe kwana 14 a can, kafin daga bisani aka dawo da shi kurkukun na Kaduna.
Karbarsa din na da alaka da sake bude gidan yarin domin karbar masu laifi da aka yi.
Kotu dai ta yankewa Sadiq Mustapha hukuncin zama gida yari har a tsawon shekara bakwai ba tare da zabin biyan tara ba, bayan da EFCC suka gurfanar da shi gaban kotun ana zarginshi da karbar naira miliyan shida da dubu dari daya bisa karya tare da gudanar da kasuwancin canjin kudi ba bisa ka’ida ba.