Kotu ta ɗage Shari’ar dake Ƙalubalantar Naɗin Sarkin Kogi
Babbar Kotun a Lagos dake ƙarƙashin kulawar Mai Shari’a Nicodemus Awulu ta ɗage Shariar Dake ƙalubalantar naɗin Abubakar Yakubu a matsayin Sarkin Ejeh na Ankpa zuwa 23 ga watan Mayu na Shekarar 2022.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yara 3 Da Wasu Mutane 6 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Abuja
Awulu ya ɗage Shariar bayan wani Lauyan dake kare wanda ake ƙara ya shigar da wani ƙorafi a gaban Kotun.
Babbar Kotun Jahar Kogi da farko ta hana Gwamnatin Jahar daga aikata bikin naɗin Yakubu a matsayin Ejeh na Ankpa.
Wannan umarni zai hana Yakubu daga “bayyana kanshi a matsayin Sarkin Ejeh na Ankpa, har sai an kammala sauraron ƙarar.”
Lauyan mai shigar da Ƙarar, Philip Abalaka yace sabon ƙorafin nada manufar neman Kotu tayi watsi da Umarnin da Kotun Jahar ta bayar
Comments 1