Kotu ta Ɗaure Ɗan Fim Shekaru 16 kan lalata da Karamar Yarinya
Wata Kotu a Ikeja mai kula da shari’u na musamman ta ɗaure Jarumin Kamfanin Shirya Finafinai na Kudu Nollywood Olanrewaju James da akafi sani da Baba Ijesha, Kan Zargin Lalata da Ƙaramar Yarinya mai shekaru 14.
Ƙamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa NAN ya ruwaito cewar Alƙaliya Oluwatoyin Taiwo, a hukuncin data yanke, ta zartarwa Baba Ijesha Hukunci kan cin zarafin ƙaramar yarinya.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Mulkin Muslumi-Kirista bai kamu ko’ina ba — Oshiomhole
An yanke mashi hukunci akan tuhuma ɗaya daga cikin 6, wanda shine cin zarafi ta hanyar fin karfi.
Alƙaliyar tace Lauyoyi sun gaza bada ƙwararan hujjoji cewa ya aikata dukkanin laifukan da ake zargin sa ya aikata.
Data ke yanke hukunci akan lamarin, Mai Shari’a Taiwo ta tura shi gidan yari na tsawon shekaru 16.
Laifukan a cewar ta, sun saɓawa sashe na 135, 137, da 261, da 202, da 262, da kuma 263 na dokar manyan laifuka ta Lagos, wanda yace hukuncin daurin rai da rai ne ga wanda suka karya ta.