Hukumar Hana Zagon Ƙasa ta Najeriya dake Shiyyar Ilori a ranar Juma’a ta nemi Kotu ta Ɗaure mutane 5 da aka kama da laifin Damfara a yanar Gizo, a gaban Mai Shari’a Muhammad Sani na Babbar Kotun Tarayya dake Zaman ta a Ilori
Waɗanda aka yanke wa hukunci akwai Ololade Olabisi daga Ƙaramar Hukumar Alimosho ta Jahar Lagos, da Issa Shahajudeen, ɗan asalin garin Offa ta Ƙaramar Hukumar Offa dake Jahar Kwara, da Segun Ajila daga Ƙaramar Hukumar Alimosho ta Jahar Lagos, da Babatunde Saheed daga Ilorin da kuma Abdulmatin Olawale daga Ƙaramar Hukumar Akinyeye ta Jahar Oyo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun baƙin cikine yadda Mutane basa iya fita neman abinci saboda matsalar tsaro — Hayab
Kafin yanke masu hukunci, dukkanin su sun amsa laifin da ake zargin su na zagon ƙasa.
Mai shigar da Ƙara daga Gwamnati ya buƙaci Kotu data duba hujjoji da yanayin shari’ar, da amsa laifin da waɗanda ake tuhuma, tare da zartar masu hukunci akan laifin su.
A zartar da hukuncin sa, Justice Sani, yace lauya mai shigar da ƙara ya gamsar da kotu, sai ya zartar masu da hukunci.
Hukuncin ya zartar da hukuncin ɗauri daban-daban, da suka haɗa da ɗaurin wata shida, da shekara ɗaya, da kuma zaɓin biyan tara.
Jojin ya bada umarnin cewa dukkanin kayayyakin da suka yi amfani dasu wajen aikata laifin da suka haɗa da wayoyi da Kwanfuyutoci da kuɗaɗen da suka samu an ƙwace su, an miƙa wa Gwamnatin Tarayya.