Wata Kotun Majistare dake da mazauni a unguwar Nomansland a jihar Kano karkashin jagorancin mai Shari’a Aminu Gabari ta bayar da umarnin kamo Muazu Magaji Ɗanbala tare da tsare shi a gidan gyaran hali, bisa zarginsa da bata sunan gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa ana kuma zargin Danbala da bata sunan ‘ya’yan gwamnan Abdul’aziz Ganduje da kuma Balaraba Ganduje, baya ga shi gwamnan kansa, a shafin sada zumunta na Facebook.
Kazalika ana kuma zargin Jamilu Shehu shima da makamancin wannan laifin.
Mutane biyun dai an gurfanar da su ne a gaban kuliya bisa zargin hada baki, cin zarafi, tayar da hankulan jama’a da bata sunan mutum wanda ya sabawa sashi na 97, 114, 391 da 399 na kundin manyan laifuffuka.
A rahoto na farko kan korafin ya bayyana cewa A ranar 26 ga Oktoba, shugaban karamar hukumar Nassarawa Honourable Auwal Lawal Shuaibu, Aranposu ya kai karar su Mu’azu Magaji Danbala da Jamilu Shehu Waɗanda dukkanin su yan Karamar Hukumar Kiru ne, gaban jami’an yan sanda na musamman.
DUBA WANNAN LABARIN: Hukumar Kwastam Na shirin samar da kudin shiga N2tn a bana
Wadanda ake zargin dai sun ki amsa laifin da ake tuhumar su, inda daga nan ne lauya Mai kariya ya nemi a bayar da belinsu.
Kotun dai ta ki amincewa ta bayar da belin wadanda ake zargin bayan da lauyan masu kara Barista Wada Ahmad Wada babban Lauyan Gwamnati yayi suka kan hakan.
Yanzu haka dai Alkalin kotun, ya umurci sashin Binciken manyan Laifuka na Rundunar ‘yan sandan da ya gabatar da takardar karar domin kotu ta duba yiwuwar bayar da wadanda ake kara beli ko kuma akasin haka.
Daga nan sai kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga Nuwamba, 2021 don ci gaba da shari’ar.