Mai shari’a Ayo Oyebiyi na babbar kotun Osogbo a jihar Osun, ya bayar da umarnin tsare Kayode Esuleke, da dansa Ifasola Esuleke, da Kola Adeosun da Akeem Idowu a gidan gyaran hali na Ilesa dake jihar, bisa zargin kashe wani mutum Mai suna Moshood Salawudeen a wani masallaci a garin Osogbo, babban birnin jihar.
An gurfanar da mutanen da ake zargi da laifuka 13 da suka hada da kisan kai, barna mai muni, kai hari, da kuma sabawa zaman lafiya, da dai sauran su
Umurnin ya ci gaba da cewa, wadanda ake tuhuma za su ci gaba da zama a gidan yarin Ilesa, har zuwa ranar 21 ga Satumba, shekarar 2021 lokacin da ake saran yanke hukunci yuwuwar bada belin su, ko Kuma a’a.
Idan za a iya tunawa, Cif Kayode Esuleke da dansa, Ifasola Esuleke, tare da wasu wadanda ake zargi sun gudanar da ibadar “Egungun Masquerade ne yayin da kuma suka kai hari ga Moshood Salawudeen, lokacin da yake sallah cikin masallaci, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Za mu yi Maraba da Jonathan zuwa APC, inji Kakakin jam’iyar
A karshe Alkalin Kotun, ya dage ci gaba da sauraron karar har izuwa ranar 21 ga Satumba, shekarar 2021.
A wani labarin Kuma na daban.
Majalisar zartarwa ta tarayya FEC ta amince da naira biliyan 38.4 don kammala wasu ayyukan hanyoyi da aka gada a jihohi biyar na tarayya kasar nan.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola ne ya bayyana haka lokacin da yake yiwa manema labarai na fadar gwamnati tarayya jawabi a karshen zaman majalisar, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ranar Laraba a Abuja.
A cewarsa, jihohin da ke cin gajiyar aikin sune Benue, Bayelsa, Anambra, Imo da Nasarawa, inda ya kara da cewa dukkan ayyukan da abin ya shafa gadar su sukayi daga gwamnatocin baya.
Shima da yake nasa jawabin ga manema labarai kan sakamakon taron, Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu ya bayyana cewa Majalisar ta amince da Naira miliyan 10.7 a matsayin kari don kammala aikin noman rani na Rima a jihar Sokoto.
“Ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya ta gabatar da wata sanarwa ga majalisar don sake duba jimlar kudin kashi na biyu na aikin ban ruwa na kwarin tsakiyar kogi,“ Wannan shine kammala aikin ban ruwa na tsakiyar Rima a Goronyo, jihar Sokoto.
“Gwamnatin soja ta fara wannan kwangilar a shekarar 1999 sannan, an kammala kashi na farko, wanda ya kunshi hekta 873.
“Don haka, wannan bayanin yana neman a sake duba farashin aikin, tare da kara kusan miliyan 10.7 don mu sami damar kammala aikin, da fatan kafin karewar wannan gwamnatin a 2023,” in ji shi.
Ministan ya ce daga cikin burin gwamnati na kammala ayyukan 116 da aka gada, 34 sun kammala.
Comments 2