Kotu ta bada belin Okorocha akan Naira Miliyan 500
Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja a ranar Talata ta sanya ƙa’idoji masu tsauri akan belin Tsohon Gwamnan Jahar Imo Rochas Okorocha wanda ke fuskantar Shari’a akan zargin karkatar da Naira biliyan 2.9 na cin hanci.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Zata Duba Yiwuwar Bayar Da Okorocha Beli A Yau
Okorocha tace zata bada belin Okorocha akan Naira Miliyan 500 tare da bada irin waɗannan kuɗaɗen a ajiye.
Haka zalika, an hana shi fita daga Ƙasar, sai dai in Kotun ta bada umarnin hakan.
Kotu ta umarci Sanatan mai Wakiltar Imo ta Yamma a Majalisar Dattijai daya ajiye Fasfo na fita Ƙasashen Waje ga Magatakardan Kotun.
Ƙari bisa ga haka, Jojin ya kuma ce dole Hukumar Kula da Shiga da fice ta Ƙasa, ta zaman to tana kula akan cewa Fasfo nashi na a hannun Kotun, kuma sai ta bada umarni sannan zai fita yabar Ƙasar.
Comments 1