Wata Kotun Majistare dake Ikeja, a ranar Talata ta bada umarnin tsare wani ɗan shekaru 29 ma’aikacin gwamnati, sakamakon yin lalata da ƴan shekara 13.
Ƴan sanda sunyi ƙarar Awaye wanda yake zaune a unguwar Agbawaye Agabdo Oke-Odo ta Jahar Lagos da laifin lalata yarinyar.
Majistare T.O. Tanimola wadda bata amince da roƙon Awaye, ya bada umarnin a cigaba da tsare shi a cibiyar gyaran hali ta Ƙiriƙiri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar ICPC Ta Garkame Tsohon Hadimin Shugaban Kasa, Obono-Obla
Tanimola ta kuma bada umarni ga ƴan sanda dasu kai lamarin ga sashen kula da hukunta ma’aikata domin neman shawarwarin doka.
Ta kuma ɗage shari’ar ya zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba domin jin shawarwarin da Sashen Hukunta Ma’aikata zai bayar.
Tunda Farko, Mai shigar da ƙara ba
ASP Victor Eruada, ya taɓa shaidawa kotu cewa ma’aikacin ya aikata lamarin a ranar 2 ga watan yuni, a gidan sa.
Yace Awaye ya shiga da ƙaramar yarinya a gidansa ya kuma yi mata fyaɗe a gidan sa, inda ya yi mata fyaɗe.
Eruada yace laifin ya saɓawa sashe na 137 na manyan laifuka na Jahar Lagos na shekarar 2015.
Sashen dai ya bada umarnin a yanke wa wanda ya aikata laifin zaman gidan yari har ƙarshen rayuwa.