Mai shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae na kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja, ya umarci hukumar tattara kudaden shiga da ta gaggauta samar da na’urar da za ta fara duba karin albashi ga wasu jami’an shari’a.
Alkalin ya yanke hukuncin ne a ranar Alhamis a karar da babban Lauyan Najeriya, Sebastian Hon. Babban Lauyan dai ya garzaya kotu ne domin neman karin albashi ga alkalan Najeriya.
A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Obaseki-Osaghae ya kuma ba da umarnin sake duba albashin ma’aikatan shari’ar da abin ya shafa a duk shekara ko kuma a kalla duk bayan shekaru biyu.
Ta kuma bayar da kudin shari’a dubu dari biyar, a madadin mai da’awar, wanda wanda akai kara na daya da na biyu da na uku za su biya.
Kotun ta kuma bayyana cewa akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da ikirari da ake yi na cewa albashin manyan alkalai da alkalai da aka yi bita a karshen shekarar 2008 baya nuna halin da ake ciki na zamani, sakamakon faduwar darajar Naira, da canjin kudi, da kuma tabarbarewar tattalin arziki gaba daya. .
Mai shari’a Obaseki-Osaghae ya kuma bayyana cewa wanda ake kara na farko (RMAFC) ya gaza yin amfani da karfin ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen duba kudaden da wadannan jami’an shari’a ke samu, shekaru 14 bayan an yi nazari na karshe a shekarar 2008.
Kotun ta bayyana sakaci, kin amincewa, da gazawar hukumar ta RMAFC wajen yin aikinta tun daga shekarar 2008.
Ta ce sakacin ya jefa jami’an shari’a talauta, tare da sanya su abin kunya, inda ta bayyana lamarin a matsayin abin kunya na kasa.
Kafin yanke hukunci kan shari’ar, Mai shari’a Obaseki-Osaghae ya yanke hukunci a kan batun, inda ya ce mai da’awar ya nuna isashen dalili don haka yana da hurumin da’awar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shari’ar dai ta ci gaba a kotun ne bayan yunkurin da majalisar dokokin kasar da majalisar shari’ar kasar suka yi a baya na ganin an sasanta ba tare da kotu ba ya ci tura.