Wata kotu ta tafi da gidanka, a Abuja, ta zartar da hukuncin biyan tara akan wasu mutane 100 da aka samu da laifin karya dokokin kiyaye yaduwar kwayar cutar korona.
Kwamitin Kar ta kwana na yaki da cutar korona ne ya kai samame a lungu da sako na Abuja domin kama mutanen da ke cikin jama’a amma basa bin dokar dakile yaduwar annobar korona ta hanyar saka takunkumi ba.
Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammed Bello, shine ya kafa kwamitin bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu akan sabuwar dokar yaki da yaduwar kwayar cutar korona.