Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci gwamnatin tarayya da hukumar yaki da masu cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, da kada su sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Abia Orji Uzo Kalu, a gaban Kotu, kan tuhumar zargi Madakalar naira biliyan 1.7 da aka yanke masa hukunci tun da farko.
Mai shari’a Kotun Inyang Ekwo ne ya ba da wannan umarni yayin da yake yanke hukunci kan karar da Kalu ya shigar yana neman a dakatar da shari’ar tasa, bisa dalilin cewa, zai zama babban hadari idan ya sake fuskantar irin wannan shari’ar, bayan an sake shi daga kurkuku.
Alkalin ya ce, babu wani cikakken umarni da Kotun ta bayar, na umarnin sake cigaba da shari’ar Kalu, yana mai cewa, hukuncin Kotun Koli bai shafi Kalu ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Kaduna za ta Rufe Kafofin Sadarwa a jihar
Sai dia Kotun ta kuma ba da umarnin a sake gurfanar da tsohon Kwamishinan Kudi a lokacin Mulkin Kalu a Abia, wato Jones Udeogu, wanda abaya aka yanke mashi hukunci tare da Kalu.
A wani labarin Kuma na daban.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta sake nazarin shirye shiryenta na gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da aka shirya yi a ranar 6 ga Nuwamba, 2021.
Kwamishinan INEC na Kasa kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Ilimin Masu Zabe, Barista Festus Okoye wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja yace yawancin cibiyoyin hukumar da suka lalace a farkon shekarar yanzu an gyara su cikin shirye shiryen zaben.
Yace Hukumar ta lura cewa an samu ci gaba mai kyau wajen gyara kayayyakin da aka lalata yayin harin ranar 23 ga Mayu, 2021 a kan ofisoshinta.
“An sake gina shagunan da aka kona kuma a shirye don karbar kayan aiki, yayin da gyaran Cibiyar tattarawa da sauran wuraren da abin ya shafa kusan an kammala”, in ji shi.
A cewarsa, an yi rajistar farko, wanda ya samo asali daga ci gaba da Rajistar Masu Zabe CVR kuma ana tsaftace shi.
“Dangane da Jadawalin Ayyukan Hukumar za ta buga Rajistar Masu Zabe da kuma jerin sunayen‘ yan takarar da za a zaba a ranar 7 ga watan Oktoba 2021. Katin masu jefa kuri’a na dindindin PVCs na sabbin masu yin rajista za su kasance a shirye don tattarawa jim kaɗan bayan 7 ga watan Oktoba.Za a sanar da masu yin rajista daidai gwargwado ta adireshin imel ɗin su da lambobin tarho lokacin da PVC ɗin su ke shirye don tattarawa.
Rana ta ƙarshe don ƙaddamar da sunayen wakilan zaɓe don zaɓen ga jami’iyun zaɓen Ƙananan Hukumomin da jam’iyyun siyasa keyi shine ranar 21 ga watan Oktoba, yayin da kamfen ɗin siyasa zai ƙare ranar 4 ga watan Nuwamba.
“Hukumar ta kuduri aniyar gudanar da kyakkyawan zabe a jihar Anambra. Muna umartar duk masu ruwa da tsaki dasu ci gaba da nuna kyawawan halaye da gudanar da ayyukansu cikin kyawawan al’adun dimokuradiyya mai sassaucin ra’ayi “, in ji shi.
Comments 1