Wata Kotun majistare dake zaune a Ado Ekiti, a jihar Ekiti, ta tura wani mutum Mai suna Olayitan Olatimehin, Mai shekara 26, gidan gyaran halin na Ado Ekiti, na tsawon kwanaki 30, bisa zargin shi da yi wata dalibar jami’ar tarayya mai shekaru 16 fyade.
Alkalin kotun Mai shari’a Saka Afunso ya bayar da umurnin tura Wanda ake zargin gidan gyaran hali ne, har sai Yan sanda sun kammala gudanar da binciken.
Da take bayyana wa yan sanda irin wahalar da ta sha, wanda abin ya faru ta ce, wanda ake tuhumar tare da abokansa a ranar 12 ga watan Satumban nan, da misalin karfe 9:30 na dare, ya yi mata fashin inda ya kwace wayarta.
Ta Kara da cewa, yayin da take kokarin amsar wayarta a hannun shi,sai ya bigeta a Kai, inda nan danan ta suma, ta kara da cewa ta farfado ne kawai ta tsinci kanta tsirara akan gadon Wanda ake zargi, tare da yage Mata dan kanfan ta, Kuma ya yi mata fyade.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka Dan Sanda bayan sun farmaki Otel a Abuja
Hakan yasa aka shigar da rahoton afkuwar lamarin a ofishin yan sanda, wanda ya kai ga cafke wanda ake kara a gari Itapa Ekiti.
Jami’in dan sanda Mai gabatar da kara Insifekta Oriyomi Akinwale, ya bukaci kotun da ta tsare wanda ake kara, domin ya ba shi damar tura kwafin karar zuwa ofishin Daraktan masu gabatar da kara DPP na jihar, don ba da shawara kan shari’a.
Akinwale ya ce laifin ya sabawa doka, kuma za’a hukunta shi a karkashin sashi na 31 na dokokin kare hakkin yaya mata na jihar Ekiti.