By Abbas Yakubu Yaura
An yankewa wani mai goyon bayan tsohon shugaban Amurka Donald Trump hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari saboda ya ci zarafin jami’an ‘yan sanda a lokacin harin da aka kai a babban birnin Amurka, wanda shi ne hukunci mafi tsanani da aka yanke a binciken tashin hankalin na ranar 6 ga watan Janairu.
An ga Robert Scott Palmer, mai shekaru 54 a cikin faifan bidiyo da hotuna sanye da rigar tutar Amurka da aka yi wa ado da facin masu goyon bayan Trump da kuma hular dake dauke rubutun “Florida for Trump” yayin da yake jefa alluna, na’urar kashe gobara da sauran abubuwa ga ‘yan sanda a wajen babban birnin tarayya.
Saivdai ya yi kokarin shiga fadar shugaban kasa amma a karshe jami’an tsaro suka harba masa barkonon tsohuwa suka mayar dashi baya.
Bayan haka, ya ci gaba da jifan jami’an, har sai da harsashin roba ya same shi tukunna ya tsagaita kai harin.
Alkalin kotun tarayya Tanya Chutkan ya ki amincewa da hujjojin Palmer na sassaucin yaran dake cikin damuwa da kuma uzuri da aka rubuta da hannu wanda yace tsohon shugaban kasar ne ya yaudare shi da wasu wadamda suka kai wa Majalisa hari, wanda ya kira “azzalumi” da kuma “matukar tsayawa kan mulki. ”
“Na gane cewa muna nufin an yi wa magoya bayan Trump karya,” ya rubuta.
Masu gabatar da kara sun nuna cewa ko da bayan karar daya yi a ranar 4 ga watan Oktoba, Palmer yaci gaba da kare ayyukansa, yana mai yiwa ‘yan sanda lakabi da masu tada kayar baya a shafin yanar gizon tattara kudade daya kafa.
“Palmer da gangan ya shiga gungun masu tayar da kayar baya da niyyar yin katsalandan ga tsarin zaben kasar,” masu gabatar da kara sun shaida wa kotun a cikin takardar yanke hukunci.
“Rikicin Palmer ya kasance don cimma burinsa na siyasa na rushe zaben dimokuradiyya da mika mulki cikin lumana.”
Hukuncin daya gabata mafi tsanani a harin na Capitol shi ne watanni 41, wanda aka yanke wa wasu mutane biyu da aka tuhume su da kawo cikas a shari’a amma ba a zarge su da cin zarafin jami’an tsaro ba.
Kazalika Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito An tuhumi fiye da mutane 700 a harin, akasarinsu da aikata kananan laifuffuka kamar shiga majalisar dokokin kasar ba bisa ka’ida ba.
Sai dai wasu gommai da dama na fuskantar hare-hare da laifukan muggan makamai da kuma hada baki, wanda zai iya kai ga yanke masa hukunci mai tsanani.