Wata kotun Majistare dake Minna a jihar Neja a ranar Alhamis ta bukaci da a sakaya mata wadansu manoma guda uku bisa zargin fashi, garkuwa da mutane da kuma fyade.
Yusuf Sule, Saleh Sarki da Juli Baushe sune manoma uku da aka gurfanar gaban kotu bisa zargin aikata laifuka guda hudun wanda ya hada da na makirci, fashi da makami. Garkuwa da kuma fyade.
Mai shigar da karar, Emmanuel Ogiri, ya shaidawa kotun cewa; wani mai suna Abdullah Bako dake kauyen Madagwa a karamar hukumar Shiroro ya shigar da kara a ranar 8 ga watan Agusta. Ogiri ya ce mai shigar da karar ya yi zargin cewa wadanda ake zargi sun zo da bindigogin gargajiya da kuma karamar bindiga suka afka ma kauyen Madagwa.
Inda ake zarginsu da yiwa wanda ya shigar da karar fashin Naira dubu 500, da kuma yin garkuwa da mata biyu da yiwa mata biyu fyade.
Mai shigar da karar ya ce wadanda ake zargi sun kuma fasa shagon siyar da kaya inda suka kwashe kayan da kudinsu ya kai Naira dubu 127.
Ogiri ya ce laifin na su ya sabawa sashe na 3 (1), 2 (1) na dokar garkuwa da mutane na Neja sashe na 298 na Fenal Kod. Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin da ake musu.
Mai shari’a, Christiana Barau, ta ce kotun ba ta da hurumin sauraren wannan karar a don haka ba ta amince da abin da suka ce ba, ta bukaci da a kai su gidan yari a matsayin ajiya. Ta nemi kuma ‘yan sanda da su aika kofin takardar zargin zuwa ga ofishin shigar da kararraki na jiha domin ba da shawarwari.
An dage sauraren karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba.