Wata babbar kotu a Legas a ranar Talata ta daure wani matashi mai shekara 31 a duniya, mai suna Uchenna Unachukwu shekaru hudu a gidan gyaran hali bisa safarar kwayar da nauyinta ya kai kilogiram 21.7.
Mai shari’a Ayokunle Faji ne ya zartar wa da Unachukwu hukuncin bayan amsa laifinsa na safarar miyagun kwayoyi.
Sai dai Alkalin ya ce; shekaru hudun wanda aka yanke wa hukuncin zai fara daga lokacin da aka kama matashin.
Mai shigar da kara, Jeremiah Aernan, ya shaidawa kotu cewa; Unachukwu ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Yuli a tashar moto ta Iddo a jihar Legas.