By Ishaq Dabai
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC reshen Ilorin, ta samu nasarar damke wani dan damfara na kafar sadarwar intanet, mai suna Jatto Sheriff Umar.
Matashin mai shekaru 21 ya kware a matsayin wanda ya kafa kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, da kuma damfarar wadanda ba a san su ba ta hanyar sadarwar yanar gizo.An yanke masa hukuncin ɗauri a gidan kurkuku saboda laifukan da suka haɗa da keɓance mutum da aikata laifuka ta yanar gizo.
Ita ma hukumar shiyyar Ilorin ta EFCC, ta tabbatar da hukunta wasu mutane hudu saboda irin wannan laifin.
Kazalika ta kama wani Jami’in Sojan Amurka na karya, mai suna Oguntoyinbo Oluwatobi Damilola, da Taiwo Akinyemi Kayode daga karamar hukumar Ekiti ta yamma na jihar Ekiti, Adebayo Adeola Mark daga Osi a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, Adedoyin Olayinka daga karamar hukumar Ilesha ta yamma ta jihar Osun da kuma wani Yusuf Alameen Abiodun daga yankin Igbo-Owu na jihar Kwara.