Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, a ranar Laraba, a Fagge, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani matashi dan shekara 21 Mai suna, Alhassan Yusuf, wanda ya amsa laifin satar kare da ya kai Darajar Naira 10,000, a gidan gyaran hali, har sai an yanke masa hukunci.
Wanda ake tuhumar wanda ke zaune a Tudun Maliki Quarters a karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano, ana tuhumarsa da laifuka biyu ne, da suka hada da aikata laifuka da kuma sata.
Wanda ake tuhumar ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Kazalika Alkalin kotun, Dokta Bello Khalid, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake kara ne a gidan gyaran hali sannan ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 3 ga watan Disamban shekarar nan, domin yanke masa hukunci.