
- Kotu ta fatattaki ƙarar da EFCC suka shigar akan tuhumar wani da almundahana da ƙudi kimanin miliyan 322
- Mai Shari’a Justice C. Akete dake Babban Kotu dake Legas ya kori ƙarar Sanata Peter N. Da ake tuhumar sa da sama da faɗin da kuɗaɗe kimanin miliyan 322.
- Kotun tace ta kori ƙarar ne bisa rashin ƙarin hujja da ita ƙungiyar EFCC ka kasa tabbatar wa.
Peter N. Ɗan jam’iyyar PDP mai wakiltar Delta ta Arewa.
Karanta:- An damƙe manyan ƴan bindiga dake Oyo
Alƙalin ya ƙara da cewa babu wani tabbacin da aka samu daga banki don tabbatar da zargin da ake masa.
Hakazalika Kotun ta bayar da belin kadarorinsa guda biyu na Golden Touch Construction limited da Suiming Electrical Ltd. A lokaci daya.
EFCC sun ce ya aikata laifin ne tun watan Mayu da Yuni na shekarar 2014.
A cewarsu Peter N. Ya mallaki katafarun kadarori da suke a Guinea House, Marine Road dake Apapa Legas da suka kai kimanin zunzurutun kuɗi miliyan 805.
A cewarsu kuɗaɗen mai kula da kamfanin Suiming Electrical Ltd. Aka turoma
Hakazalika kamfanin Suiming Electrical an zarge shi tun 14 ga watan Mayun shekarar 2014 tare da Peter N. dan Kamfanin Golden Touch da almundahana.
Waɗanda ake zargin an damƙasu a shekarar 2018 a gaban alƙali Muhammed Idris inda a yanzu ai maida shi Kotun Appeal.
Sannan an ƙara gabatar dasu a gaban Alƙali Aneka a watan Oktoba 5, shekarar2018.