Kotun Majistare da ke gudanar da zamanta a garin Minna ta bada umurnin kulle wani matashi dan shekara 20 mai sana’ar babur, Mustapha Aliyu a kan zargin jefa jaririnsa mai wata uku cikin ruwan rafi.
An caji Aliyu da laifin kisa wanda hakan ya sabawa sashi na 221 na Fenal kod. Lauyan da ya mika karan zuwa kotu, ASP Daniel Ikwoche, ya bayyanawa kotun cewa Amina Zakaria, mahaifiyar jaririn ta mika karan zuwa ga hukumar Civil Defence a ranar 8 ga watan Satumba.
Ikwoche ya ce mahaifiyar ta kasance tana zama a kauyen Keranbadi dake karkashin karamar hukumar Borgu a jihar Neja inda ta ce ta samar da cikin shege ne ga wanda ake zargi.
Lauyan ya ce shi wanda ake zargi ya ziyarce ta da misalin karfe 9:30 na yamma a ranar 7 ga watan Satumba sannan ya tafi da jaririn. Ikwoche ya ce shi wanda ake zargi ya dauke jaririn zuwa kauyensa, Tamanai inda ya jefa jaririn cikin rafi a nan ne jaririn ya mutu.
A yayin da aka karantawa wanda ake zargi da aikata laifin, ya amince da laifin da ake zarginsa da shi sannan kuma ya roki kotun da ta masa sassauci wajen yankin hukuncinta.
Alkalin kotu, Hauwa Yusuf ta ki amincewa da hakan inda ta ce kotun ba ta damar yanke hukuncin karar. Yusuf ta umurci lauyar da ya mika karan zuwa kotun da ya kai kwafin takardun karar zuwa ga ofishin Darakta masu laifuka na jihar (DPPs) domin samun shawara a kan yadda za shawo kan lamarin.
Daga nan sai ta daga karar zuwa 10 ga watan Oktoba 2019.