Wata kotun soji a kasar Tunisia ta yanke hukuncin dauri ga wasu ‘yan majalisar dokokin kasar hudu bisa zargin cin zarafin ‘yan sanda a bara.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Saif Eddine Maklouf, wanda ke jagorantar jam’iyyar Karama a majalisar dokokin da aka rusa.
Wani fitaccen mai sukar shugaba Kais Saied, na daya daga cikin wadanda aka yanke masu hukuncin daurin watanni biyar a gidan yari – wasu ‘yan jam’iyyar uku sun samu irin wannan hukunci.
A wani labari Kuma na daban
Da Dumi-dumi: Sojoji Sun Harba Alburusai, Don Tarwatsa Daliban Masu Zanga-zangar Nuna Adawa Da Yajin Aikin ASUU
Jami’an soji sun tarwatsa daliban jami’o’i daban-daban a jihar Ondo da ke zanga-zangar nuna adawa da yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU.
An ce sojojin sun bude wuta ne domin fatattakar daliban daga babbar hanyar Ilesha/Akure a ranar Talata.
Daliban Wadanda sun kasance daga Jami’oin Fasaha ta Tarayya da ke Akure, FUTA, Jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba-Akoko, AAUA, da Jami’ar Fasaha ta Olusegun Agagu da ke Okitipupa, OAUSTECH sun fito kan tituna da nuna rashin jin dadin su.
Daliban dai tun a ranar Litinin din da ta gabata suka tare babbar hanyar inda suka dakile zirga-zirgar ababen hawa.
Kazalika Daliban da suka yi zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan halin gwamnatin tarayya kan lamarin da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU, sun yi dandazo ne a kofar Arewa ta jami’ar FUTA da kuma shingen hanya inda suka tare hanya domin yin rajistar isar da kokensu.
An tattaro cewa sojojin da ba na birgediya ta 32 na jihar bane, Wadanda suka zo wucewa ta kan hanyar ne lokacin da daliban da suke zanga-zangar suka hana su wucewa ta babbar hanyar da ke bakin Titin.
A cewar wasu daga cikin daliban da suka yi kaca-kaca domin tsira da rayukansu, sojojin da ke tahowa daga karshen titin Ilesha sun afka wa daliban tare da lalata musu kayansu.